Take a fresh look at your lifestyle.

Chadi Ta Yi Afuwa Ga ‘Yan Tawaye 380 Da Aka Daure Kan Mutuwar Tsohon Shugaban Kasar

Aisha Yahaya, Lagos

31

Shugaban rikon kwarya na kasar Chadi, Mahamat Idriss Deby, ya yi wa ‘yan tawaye 380 afuwa daga kungiyar, The Front for Change and Concord in Chadi (FACT).

 

 

Sun kasance cikin rukunin mutane 400 da aka yankewa hukuncin daurin rai da rai a ranar Talatar da ta gabata, dangane da mutuwar mahaifinsa, wanda ya dade yana mulkin kasar, Idriss Deby Itno a shekarar 2021.

 

 

An kashe shi ne a lokacin da ya ziyarci dakarun da ke yaki a fagen daga a arewacin Chadi.

 

 

A farkon wannan shekarar ne kungiyar ta kaddamar da farmaki daga sansanonin da ke Libya.

 

 

An dai samu ‘yan tawayen da laifin ta’addanci, da zagon kasa ga tsaron kasa, da jefa rayuwar shugaban kasar cikin hadari, da daukar yara kanana, da dai sauransu.

 

 

Shugaban kungiyar ‘yan tawayen da ke gudun hijira, Mahamat Mahdi Ali, wanda aka yi masa shari’a kuma aka yanke masa hukunci ba ya cikin shirin afuwar da shugaban kasar ya yi.

 

Idriss Deby, wanda gwamnatin mulkin soja ta nada bayan mutuwar mahaifinsa, ya yi tattaunawar sulhu da kungiyoyin ‘yan tawaye daban-daban tun daga lokacin.

 

Sai dai FACT ba ta shiga ba tana mai cewa hukumomin rikon kwarya na bukatar su fara nuna alamun zaman lafiya, gami da sakin fursunoni.

 

 

“Ya yi alkawarin gudanar da zaben dimokuradiyya bayan watanni 18, wanda zai kasance a watan Oktoba na 2022, amma yanzu ya ce za a kada kuri’a a 2024”.

 

 

Wannan ya haifar da mummunar zanga-zangar adawa da gwamnati inda akalla mutane 60 suka mutu sannan aka kama wasu daruruwa.

Comments are closed.