Akalla faren hula shida ne suka mutu sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai a babban birnin kasar Afganistan a ranar Litinin, kusa da wani shingen binciken jami’an tsaro zuwa ma’aikatar harkokin wajen kasar.
Kakakin ‘yan sandan Kabul Khalid Zadran ya ce “A dandalin Malik Asghar… an gano wani dan kunar bakin wake kafin a kai ga inda aka kai harin a wani shingen bincike aka kashe shi, amma bama-baman da ke jikinsa sun tashi,” in ji kakakin ‘yan sandan Kabul Khalid Zadran.
Zadran ya ce mutane da dama sun jikkata ciki har da jami’an tsaron Taliban uku.
Sai dai bai bayyana sunan wanda aka kai harin ba, amma fashewar ta auku ne a wani wuri mai cike da cunkoson jama’a a kusa da wani shingen binciken ababen hawa da ke gadin wani katafaren titi da ke dauke da gine-ginen gwamnati da dama ciki har da ma’aikatar harkokin wajen kasar.
Asibitin gaggawa na kusa, wanda wata kungiya mai zaman kanta ta Italiya ke gudanarwa, ya karbi raunukan marasa lafiya 12 da gawarwaki biyu, in ji darektan kasar.
Kabul da wasu yankunan birane na fuskantar hare-hare da dama a ‘yan watannin nan, wadanda wasu daga cikinsu mayakan IS ne suka dauki alhakinsu.
Karanta kuma: Kabul: Harin kunar bakin wake a cibiyar jarrabawa ya kashe mutane 19
Wani fashewa a cikin watan Janairu ya kashe akalla mutane biyar tare da raunata da dama a ma’aikatar harkokin wajen kasar yayin da ma’aikata ke fitowa daga ginin a karshen an tashi daga aiki.
Gwamnatin Taliban ta ce ta mayar da hankali ne wajen tabbatar da tsaron kasar, sannan ta kai hare-hare da dama kan wadanda ake zargin ‘yan kungiyar IS ne a cikin ‘yan makonnin nan.
Lamarin na ranar litinin ya faru ne a daidai lokacin cin abinci a lokacin da birnin ke cike da cunkoson jama’a yayin da ma’aikatan ofishin gwamnati ke tashi da wuri domin gudanar da azumin watan Ramadan.
Comments are closed.