Take a fresh look at your lifestyle.

ABBA KABIR YA KARBI TAKARDAR SHEDAR LASHE ZABEN GWAMNAN KANO

Yusuf Bala Nayaya,Kano.

116

Zababben gwamnan karkashin inuwar jam’iyyar NNPP Injiniya Abba Kabir Yusuf bayan karbar takardar lashe zabe a wannan Laraba a ofishin na INEC da ke Kano ya bayyana yafiyarsa ga wadanda suka bata masu.

 

 

Abba Kabir Yusuf bayan yaba wa jami’an tsaro kan irin rawar da suke takawa wajen tabbatar da tsaro na lafiya da dukiyoyin al’umma ya kuma ja hankalin wasu daga cikin jami’an tsaro da su guji cusa kansu a cikin harkoki na siyasa ko bari a yi amfani da su don muzgunawa wani.

 

 

“ Za mu yi kokari mu hana irin wannan abu da ya faru a shekarar 2023. Akwai wasu kalilan na jami’an tsaro da suka sa hannu dumu-dumu kan harkoki na siyasa.Bamu so jami’an tsaro al’ummar jihar Kano su rika gudunsu ba. Kada su bari ana kallonsu a harkoki wadanda bana mutunci ba.Tun da Allah Ya bamu, yau mune, mun yafe wa kowa.”

 

 

A cewar Abba Kabir Yusuf, gwamna babu abin da yake so face ganin jiharsa ta bunkasa al’umma su zauna lafiya, tattalin arziki ya samu tagomashi don haka ya nunar da bukatar hada kai da sauran jam’ian tsaro da masu sarautar gargajiya da ‘yankasuwa. Ya kuma yaba wa kwamishinan ‘yansanda na jihar da jami’an tsaro na farin kaya, da sojoji, da hukumar ta INEC, haka nan ya yaba wa jagoran tafiyar ta Kwankwasiyar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ya bayyana a matsayin gwarzon jagora.

 

 

Al’umma a jihar ta Kano dama ‘yan jam’iyyar ta NNPP mai kayan dadi sun bayyana farinciki bayan da zababben gwamnan Abba Kabir Yusuf ya karbi takardar shedar lashe zaben gwamnan da aka yi ranar 18 ga watan nan na Maris.

 

 

Injiniya Abba Kabir Yusuf dai zababben gwamnan na jihar Kano ya bayyana cewa nasararsa ta kowace, kuma yayi kira ga duk masu ruwa da tsaki kan shaanin mulkin jihar ciki kuwa har da babban abokin hamayyarsa da suka yi takara Dakta Nasiru Yusuf Gawuna na APC su ajiye banbanci na siyasa a yi masa mubayi’a, azo a tafi tare don ciyar da jihar ta Kano gaba, wanda kuma hakan ne ta faru Dakta Gawunan a wani sakon murya ya nunar da mika wuyansa ga zababben gwamnan.

Comments are closed.