Zababben Gwamnan Jihar Kano Ya Nada Sunusi Bature Babban Sakataren Yada Labarai
Yusuf Bala Nayaya,Kano.
Zababben gwamnan jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya Injiniya Abba Kabir Yusuf ya nada Sunusi Bature Dawakin Tofa a matsayin babban sakataren yada labaran shi har tsawon lokaci da za a dauka har a mika masu mulkin Kano.
A wasika da shugaban kwamitin shirye-shirye na kaiwa ga mulki ya rattabawa hannu a madadin gwamna, ya bayyana mikamin da aka ba wa Mista Bature cewa, “wannan mukami ya dace da shi duba da irin kwarewar aikin shi da sadaukar da kai da biyayya ga aiki tukuru da ya nuna tun daga shekarar 2019.”
Sunusi Bature ya kasance kwararre kan harkokin hulda da jama’a da harkoki na sadarwa da kulla alaka da kwararru a tsawon shekaru 19 na aiki da yayi dahukumomi da kungiyoyi na kasa da kasa da fannoni masu zaman kansu da kafafan yada labarai a Najeriya.
A shekarar 2008 Bature ya lashe kyautar ilimi ta Cambridge wacce ke nuna kwarewa a aikin jaridar masu binciken kwakwaf. Yayi aiki da hukumomi da kungiyoyi na kasa da kasa kamar ofishin Birtaniya mai lura da harkokin kasashe rainon Ingila na (FCDO) da Asusun ba da Tallafi na Amurka USAID da Gidauniyar Bill and Melinda Gates da sauransu. Bature yayi karatu a fannin aikin jarida da wasu fannoni na ilimi da ya kai har matakin digiri na biyu a jami’oi da manyan makarantun ilimi da ke a arewaci da kudancin Najeriya har ma da ketare.
Leave a Reply