Take a fresh look at your lifestyle.

Dr Kailani Mu Ka Sani A Matsayin Shugaban AASG – Maryam Danjaki

Musa Aminu, Abuja

0 279

Gamayyar kungiyoyin magoya bayan jam’yyar APC wato APC Amalgamated Support Group  ko kuma AASG a takaice, sun bukaci al’umma da su kasance masu taka tsantsan wajen tantance labaran da suke karantawa a kafar yada labarai na zamani wato social media a turance, wannan kira ya biyo bayan wani guntun faifan bidiyo da wadansu ke yadawa cewa shugaban jam’iyyar APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu, ya sake jaddada Dr Nasiru Ladan a matsayan shugaban kungiyar ta AASG.

Mataimakiyar shugaban kungiyar Hajiya Maryam Danjaki  ta ce tun ranar tara ga wata febrerun wannan shekarar ta 2023 suka sauya shugabancin kungiyar daga hannun Dr Nasiru Ladan zuwa ga Dr Kailani Muhammad kamar yadda dokokin gudanarwar kungiyar ya basu dama.

“dukkanin kungiyoyin goyon bayan jam’iyyar APC kan su a hade ya ke kuma suna magana ne da murya daya don haka tun da su ka canja shugabanci kungiyar sakamakon zargin cin amanar Jam’iyya da suka yi wa tsohon shugaban da kuma gudanar da harkokin kungiyar da yake yi shi daya tilo, babu wani mai kishi da son ci gaba da zai koma ya hada kai da tsohon shugaban domin cimma bukatun kai. Mu dai Dr Kailani muka sani a matsayin shugaban mu’’

Danjaki  ta bukaci al’umar Najeriya musamman mambobin kungiyar su ta APC Amalgamated support Group da su yi watsi da faifen bidiyon da ake yadawa wadda a cewarta  ba shi da sahihanci ko kadan. Ana amfani da yan bani na iya da ke wa aikin jarida karan tsaye ne domin shigar da rudani a tafiyarsu, saboda tana da yakinin cewa shugaban jam’iyyar APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu a matsayinsa na dattijo kuma kwararre a fagen siyasa ba zai taba mayar da hannun agogo baya ba a tsakaninsu.

A gefe guda kuma, mataimakiyar shugaban kungiyar ta AASG ta ce tuni shirye-shiryensu ya yi nisa dangane da bukukuwan da suke fatan gudanarwa a lokacin mika mulki ga zababben shugaban Najeriya da mataimakinsa, Bola Ahmed Tinubu da Sanata Kashim Shatima.

A. K

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *