Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnan Jihar Adamawa Ya Taya Mace Ta Farko Na Sojan Ruwa Murna

0 239

Gwamnan jihar Adamawa Umaru Fintiri ya taya Jamila Malafa murnar samun karin mukamin Rear Admiral, a rundunar sojojin ruwan Najeriya.

Ita ce ta farko a daukacin yankin Arewa da rundunar sojojin ruwan Najeriya ta samu karin girma a wannan matsayi.

Babban hafsan sojin ruwa ya yi wa Admiral Jamila wanda ya fito daga karamar hukumar Gombi ado a Abuja a hukumance.

Gwamna Fintiri ya bayyana cewa, Admiral Jamila a tsawon shekarun da suka gabata ta nuna kwazonta a wannan sana’a, inda ya kara da cewa daukakar da ta yi a baya-bayan nan ya dace da kuma zaburarwa ga sauran matan da suke kokarin yin suna a wannan sana’a.

“Ba ni da tantama a raina cewa hular ta dace da wannan mace mai karfi da aka haifa a Adamawa, Rear Admiral Jamila. Ta na da kwazon da ta yi fice a aikin sojan ruwa, wanda hakan ya sa ta samu daukaka har zuwa kololuwar sana’a,” inji Gwamnan.

Ya kuma bukaci babbar jami’a ta farko daga jihar da ta kawo mata kwarewa, ba kawai wajen ciyar da rundunar sojin ruwa gaba ba, har ma da sojojin Najeriya da na jiha.

“Ina kira gare ku da ku ga daukakar ku a matsayin wanda ya zo a daidai lokacin da rayuwarmu ta kasa ke da bukatar Sojoji su kara kula da ci gaban kasa wajen taka rawar da ta taka na kare kasa da muradunta a tsarin dimokuradiyya,” in ji shi.

Gwamnan ya kuma baiwa Admiral kwarin gwiwar ci gaba da wakiltar jihar Adamawa da kyau tare da yi mata fatan samun nasara a aikin sojan ruwa.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *