Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnatin Jihar Kano Ta Kafa Kwamitin Mutum 17

0 211

Gwamnatin jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya ta kafa kwamiti mai mambobi 17 da zai yi aikin mika gwamnati daga  gwamnati jam’iyyar APC bisa jagora in Dr. Abdullahi Umar Ganduje zuwa gwamnati jam’iyyar NNPP bisa jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf.

 

Majalisar zartarwar gwanatin ta kuma amince da wani karamin kwamiti mai mambobi 100 da za su fitar da bayanai daga ma’aikatu da hukumomi daban-daban na gwamnatin jihar ta Kano.

 

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, shi ne ya sanar da hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai kan sakamakon taron majalisar na mako-mako da aka gudanar a zauren majalisar da ke gidan gwamnatin jihar Kano, ya ce ana sa ran zababben gwamnan zai ba da wakilai uku a babban kwamitin.

 

Wannan kwamiti  zai yi aiki ne karkashin jagorancin sakataren gwamnatin jiha Alhaji Usman Alhaji.

 

A cewar kwamishinan yada labaran da harkoki cikin gida gwamna Ganduje zai kaddamar da kwamitin a ranar Talata da karfe biyu na rana a dakin taro na Africa House da ke gidan gwamnatin Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *