An bayyana cewa tattaunawa da tuntubar juna na da mutukar mahimmanci wajen gina kasa, Daraktan Kungiyar Tuntubar Juna ta UFUK, Aman Riaz shi ya bayyana haka a yayin wata walimar buda baki da kungiyar ta shirya wa wasu manema labarai da suka hada da Musulmai da Kiristoci a Legas da ke Kudu maso yammacin Najeriya.
Ƙungiyar mai zaman kanta, wadda ake kira UFUK Dialogue ta bayyana wasu muhimman abubuwa waɗanda ta ce dole ne a samar da su don tabbatar da samun al’umma ta gari.
A cewar kungiyar, zaman lafiya da hakuri da kuma tuntubar juna sun kasance muhimman halaye wadanda dole ne ‘yan kasa su runguma domin samun zaman lafiya a tsakanin al’uma da kuma ci gaban kasa a kowane lokaci.
Daraktan ya kara da cewa tattaunawa da tuntubar juna a ko da yaushe sune tubali na samun zaman lafiya sun kasance koyaushe, kuma kuma dabi’a ce da ake bukatar ko wanne Dan kasa ya runguma.
Har wa yau ya ce, “Aikin samar da zaman lafiya yana bukatar ma’aunin da ya wuce kowace akida, tsarin siyasa, da duk wani yunkuri na addini ko hukuma.”
Yayin da yake tattaunawa da ‘yan jarida, daraktan ya sake nanata cewa UFUK Dialogue ta damu kwarai game da mafi girman amfanin bil’adama.
“A cikin Tattaunawarmu da tuntubar juna ta wannan kungiya ta UFUK, muna tsayuwa irin ta daka wajen ganin an samu zaman lafiya da ƙauna, haƙuri da tausayi a tsakanin al’uma da kuma samun goyon bayan adam da mafi kyawun ɗan adam,” a cewar Riaz.
Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa a yayin tattaunawar, Mista Sunday Odibachy, editan jaridar National Daily, ya yaba wa UFUK bisa gudanar da wannan taro. Sai dai ya bukaci kungiyar da ta kara himma wajen wayar da kan jama’a, musamman a yankin arewacin Najeriya inda tsatsauran ra’ayin addini ya zama ruwan dare.
Shugabannin addinai da masu rike da sarautun gargajiya na da irin rawar da za su iya takawa wajen samun haɗin kai da kuma bai wai Hukumomin jihohi kwarin gwiwa wajen dakile duk abubuwan da ke taimakawa ta’addanci a kasar.
Mista Kola Aliu na jaridar Leadership ya bukaci UFUK da ta kara tsunduma cikin harkokin watsa labarai na kasa-da-kasa da shirye-shiryen musayar bayanai ga ‘yan jarida da editoci, don inganta wayar da kan jama’a da musayar ra’ayi.
Shi ma da yake nasa jawabin, Mista Paul Ogbuokiri na New Telegraph ya yi kira da a kara hada kai da kafafen yada labarai a kasar, yana mai jaddada cewa, akasarinsu ba su da masaniya kan manyan ayyuka da gudummawar da kungiyar ke bayarwa ga al’uma.
Ya kuma nuna jin dadinsa ga kungiyar da ta hada kan kafafen yada labarai domin liyafar buda baki ba tare da la’akari da banbancin addini ko kabila ba.
Sauran ‘yan jaridar da suka halarci walimar buda bakin sun hada da Mrs Opeyemi ta Media Hallmark, Sulyman Hussain na New Telegraph da Mista Ikechi Izeako mai wakiltar Daily Independent.
An dai kafa ita wannan Kungiyar ne ta Tattaunawa ta UFUK don inganta dabi’ar zaman da fahimtar juna a tsakanin al’uma. Har wa yau kungiyar na mai da hankali kan tattaunawa da ayyukan zaman lafiya a matakan ilimi da tunani a tsakanin jama’a daban-daban.
Abdulkarim Rabiu
Leave a Reply