Take a fresh look at your lifestyle.

NPC Ta Baza Jami’an Tsoro 18,000 Don Gudanar Da Bikin Easter Cikin Lumana

Musa Aminu, Abuja.

0 273

Kungiyar dake taimakawa jami’an tsaro domin wanzar da zaman lafiya a Najeriya wato, Nigerian Peace Corps ko kuma NPC a takaice, ta taya mabiya addinin kirista murnan bukin Easter na wannan shekarar, kungiyar ta kuma yi alkawarin baza dubban jami’anta a jihohi talatin da shida hadi da Abuja fadar mulkin kasar domin ganin an gudanar da bukin cikin kwanciyar hankali da lumana.

Shugaban kungiyar a Najeriya Dakta Mustafa Muhammad Abubakar shi ne  ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da gidan Rediyon Muryar Najeriya a ofishinsa dake Abuja dangane da  ci gaba da kungiyar ta samu a yan kawanakin nan kan abun da ya shafi tabbatar da dokar da zata sanya kungiyar cikin hukumomin gwamnatin Najeriya.

Dr Mustafa Ya ci gaba da cewa “ Tuni mu ka baza jami’an mu kimanin dubu goma shatakawas (18,000) a fadin jihohin Najeriya talatin da shida hadi da Abuja fadar mulkin kasar nan domin ganin mabiya addinin kirista sun gudanar da bukukuwan su ba tare da tashin ta shina ba, saboda babban burin mu shi ne zaman lafiya a tsakanin yan kasa don haka muka baza jami’an mu, kuma muna jaddada kira ga matasa da su guji duk wanda ke son yin amfani da su domin tada husuma a daidai wannan lokaci dama bayan sa”

Kazalika, shugaban kungiyar ya yabawa shugabancin majalisar dokokin Najeriya na tara bisa daidaita rahotannin kwamitinsu da suka yi kwanan nan domin ganin sun mika ma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta yadda zai rattaba hannu a dokar kungiyar ta NPC ba tare da wata-wata ba.

Bugu da Kari, ya bukaci masu ruwa da tsaki da su tabbatar sun yi dukkanin mai yiwuwa ta yadda za a tabbatar da dokar kafin wa’adin gwamnati mai ci ya kare.

Tun da fari dai, Dakta Mustafa ya umurci jami’an kungiyar da su kasance masu atisayen motsa jiki domin samun karin kuzari, kana ya shawarci al’umar Najeriya da su guji duk wani ko wata dake karbar kudade a hannun su da sunan sama masu guraben ayyuka a kungiyar, ya kuma yi kira  ga daukacin yan kasa da su ci gaba da yin adduo’I ga gwamnati mai ci da kuma mai shirin karbar mulki domin samun ci gaba mai dorewa a fadin kasar baki daya.

AK

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *