Kwamitin da aka dorawa alhakin aikin karɓar mulkin Kano daga jam’iyyar APC karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje zuwa ga Injiniya Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a watan Mayu 2023, ya shawarci dukkanin shugabannin kananan hukumomi 44 da manyan ma’aikatansu da su guji yin amfani da kudaden kananan hukumomin su ta hanyar ci gaba da sabawa doka.
A cewar shugaban kwamitin karbar mulkin Dakta Abdullahi Baffa Bichi: ” A kwai zargin ana shirin amfani da kudaden kananan hukumomi wajen daukar nauyin wata jam’iyya a kammala wasu zabuka na ‘yan majalisar tarayya da jiha a inda basu kammala ba ranar 15 ga watan nan na Afrilu, a wasu kananan hukumomi a jihar ta Kano, wanda yin hakan ba dai-dai bane kuma ya sabawa doka.” Inji Dr.Bichi.
A cewar Dakta Bichi daukar kudaden al’ umma don daukar nauyin wata jam’iyya, gwamnati mai jiran gado ba za ta lamunta ba don haka a guji yin hakan.
Leave a Reply