Kidayar Jama’ar Kasa: Gwamnatin Jihar Katsina Ta Kaddamar Da Kwamitin Wayar Da Kan Al’umma
Kamilu Lawal,Katsina.
Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya kaddamar da wani kwamiti domin wayar da kan jama’a dangane da aikin kidayar jama’a na kasa mai zuwa.
Kwamitin na matakin jiha wanda gwamnan ya kaddamar a gidan gwamnatin jihar na da mambobi ashirin 24 da zasu gudanar da aikin kalkashin jagorancin mataimakin sa tare da taimakon kwamishinan hukumar zaben ta kasa mai kula da jihar Katsina engr. Bala Almu Banye.
Gwamnan wanda mataimakin nasa Alhaji Mannir Yakubu ya wakilta wajen kaddamarwar ya bayyana cewa a matakin kowace karamar hukuma dake jihar ma an kafa irin wannan kwamiti domin samun nasarar aikin kidayar.
Ya bukaci yan kwamitin da su gudanar da aikin yadda ya kamata domin tabbatar da cewa dukkanin al’ummar jihar sun fahimci abinda ya kamata su sani da kuma wanda ake bukata daga garesu dangane da aikin kidayar jama’ar dake tafe
Yace,“Kuna sane da mahimmancin da kidayar jama’a take dashi ga cigaban kowace kasa, duk kasar da take son ganin cigaba sai ta tantance yawan jama’ar da take dasu domin taimaka mata wajen gudanar da tsare tsaren cigabanta yadda ya kamata”,.
Aiyukan da aka dora ma kwamitin sun hada gudanar da shirya gangamin wayar da kan jama’a akan aikin kidayar jama’ar da gidaje dake tafe a fadin kasar nan da tsarawa hadi da aiwatar da dabarun wayar da kan jama’ar a matakan kwamitin
Kazalika kwamitin na da alhakin tabbatar da cewa an shigo da masu ruwa da tsaki wajen aiwatar da aikin dake gaban su.
Tun farko, a nasa jawabin, kwamishinan hukumar kidayar na kasa mai kula da jihar Katsina engr. Bala Banye ya bayyana cewa domin taimaka yan kwamitin wajen gudanar da aikin su za’a shirya masu wani taron bita domin ilmantar dasu akan shirye shiryen hukumar na aikin kidayar mai zuwa cikin nasara.
Ya tabbatar wa al’umma da dukkanin masu ruwa da tsaki cewa hukumar ta kammala dukkanin tsare tsare da suka wajaba domin gudanar da aikin kidayar cikin kwarewa kuma yadda ya kamata.
Mambobin kwamitin sun hada jami’an gwamnati da kungiyoyin kwadago da na farar hula da kuma shugabannin kafafen yada labarai hadi da wakili daga hukumar wayar da kan al’umma ta kasa(NOA)
Sauran wadanda kwamitin ya kunsa sun hada da shugabannin al’umma da wakillai daga kungiyoyin addini da sauran kwararru hadi da sauran masu ruwa da tsaki
Da yake jawabi a wajen taron shugaban gamayyar kungiyoyin fararen hula na jihar Katsina Kwamred Abdullahi ya yabama gwamnatin jihar Katsina bisa irin gudummuwar da take badawa wajen ganin ayyukan kidayar sun samu nasara
Ya bukaci dukkanin masu ruwa da tsakin su bada irin gudummuwar da ta dace domin cimma nasarar da ake bukata.
Leave a Reply