Take a fresh look at your lifestyle.

Sudan Ta Yi Zanga-Zanga Kan Mulkin Sojoji

0 153

An gudanar da zanga-zangar neman demokradiyya a sassa da dama na kasar Sudan a ci gaba da nuna bacin ransu kan ci gaba da mulkin soji.

 

Masu zanga-zangar sun kuma yi bikin zagayowar ranar zaman dirshen da aka yi a shekarar 2019 wanda ya kai ga hambarar da tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir.

 

Rahoton ya ce tun bayan da sojoji suka mamaye madafun iko, an shafe watanni ana tattaunawa, kuma tun da farko ya kamata a sanya hannu kan yarjejeniyar kaddamar da wani sabon sauyin siyasa zuwa dimokuradiyya.

 

Sai dai kuma an sake jinkiri saboda rashin jituwa tsakanin jami’an tsaro.

 

Wani yanki na tashe-tashen hankula shi ne shirin haɗa wata ƙungiya mai ƙarfi ta soji da aka fi sani da Rapid Support Forces cikin runduna ta yau da kullun.

 

 

BBC/Aisha Yahaya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *