Shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya karbi bakuncin takwaransa na Venezuela Nicolas Maduro a Algiers.
Shugaban na Kudancin Amurka ya isa kasar da ke arewacin Afirka a yammacin Laraba, don abin da kamfanin dillancin labarai na Aljeriya ya kira ziyarar aiki ta kwanaki biyu.
Kasashen biyu sun amince da karfafa hadin gwiwarsu ta fuskar tattalin arziki, Tebboune ya sanar a wata sanarwar hadin gwiwa cewa, nan ba da jimawa ba za a fara jigilar jirage kai tsaye tsakanin Algiers da Caracas.
Aljeriya da Venezuela mambobi ne na kungiyar OPEC ta kasashe masu arzikin man fetur kuma gwamnatocinsu sun bayyana fatansu na yin aiki kafada da kafada a fannonin mai da iskar gas.
Don yin hakan, Maduro ya sanar da cewa, za a sake farfado da hukumar hadin gwiwa ta kasashen Aljeriya da Venezuela domin tsara sabuwar taswirar hadin gwiwa ga kasashen biyu.
Ziyarar Maduro a Aljeriya ta biyo bayan wt ziyara da ya kai kasar Turkiyya.
Hakan kuma ta zo ne kwana guda kafin a fara babban taron shugaban kasar Amurka.
Leave a Reply