Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a daren ranar Alhamis ya karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Bola Tinubu a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Tinubu, wanda ke tare da Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da dan uwansa, Wale Tinubu, sun isa gidan gwamnatin da misalin karfe 8:42 na dare (lokacin gida).
Da yake magana da manema labarai bayan taron, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya sha alwashin ci gaba da aiwatar da nasarorin da Shugaba Buhari ya samu idan ya lashe zaben shugaban kasa a 2023.
Ya kuma yabawa shugaban kasar bisa yadda ya samar da daidaito wajen gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar, inda ya kara jaddada cewa ya sha alwashin zai goyi bayan tsarin dimokuradiyya kuma ya tabbatar da hakan a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar.
“Ya yi alkawari ga daukacin kasar da ma duniya cewa zai gina ginshikin gaskiya da daidaito da kuma bai wa ko wane dantakara damar adama da shi a zaben. Zai jajirce wajen bin ka’idoji da dabi’u na demokradiyya kuma ya yi hakan.
“Bai zabi kowa ba, bai dora kowa ba, bai kuma yi wani yunkuri na yin walawala da tsarin zaben don fifita wata kabila akan wata. Ya kasance mai tsayin daka, mai rikon amana, ya kasance abin dogaro kuma ya kasance shugaba” in ji Tinubu.
Tallata Dantakara
Dangane da batun yakin neman zabensa a mtsayain dantakarar shugaban kasa, kawai ya ce: “Ina da hazaka, na kware, tun daga kamfanoni masu zaman kansu, har zuwa na gwamnati kuma a shirye nake in fara wannnan tafiya rana guda ba tare da bata tarihin ci gaba ba, gaskiya wannan shi ne a bin day a ragemin da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya damka mani Mulki.
“Ya kamata duk ‘yan jam’iyyar APC su yi murna kadan ; Yanzu muka fara aiki tukuru gabanin samun nasarar jam’iyyarmu abu ne mai wahala kuma za mu yi nasara.”
Da aka tambaye shi kuma zabin abokin takararsa, Tinubu ya ce “Ba zan gaya muku haka ba. Wannan hakkina ne; yana cikin zuciya ta.”
AK/LADAN
Leave a Reply