Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnatin Najeriya Ta Alakanta Harin Ondo Da ISWAP

Timothy Choji, Abuja

0 462

Gwamnatin Najeriya ta ce harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a ranar Lahadin da ta gabata a cocin St. Francis Catholic Church, da ke Owo, jihar Ondo, a kudu maso yammacin Najeriya, wanda ya yi sanadin mutuwar masu ibada, yana da alaka da kungiyar dake fafutukar kafa Daular Islama a yammacin Afrika, ISWAP.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa a karshen taron majalisar tsaron kasar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Ministan ya ce an umurci ‘yan sanda da su binciki wadanda suka aikata wannan aika-aika domin gurfanar da su a gaban kuliya.

Mista Aregbesola ya ce an gano tambarin kungiyar ISWAP a wurin da aka kai harin, yana mai shan alwashin gurfanar da su gaban kotu.

Ministan ya kara da cewa kungiyar ta ISWAP na da burin tunzira ‘yan Najeriya fada da juna ta hanyar wannan harin domin ganin ya zama yakin kabilanci da addini.

Ya ci gaba da cewa majalisar ta damu matuka kan yadda aka aikata ta’addanci a jihar Sokoto da kuma babban birnin tarayya, inda aka kashe mutane biyu, ya kara da cewa gwamnatin Najeriya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen samar da isasshen tsaro ga ‘yan kasar a fadin kasar.

 

LADAN

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *