Take a fresh look at your lifestyle.

Ranar Dimokuradiyya: Shugaba Buhari Zai Yi Wa ‘Yan Najeriya Jawabi A Ranar Lahadi

0 421

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga ‘yan Najeriya a ranar 12 ga watan Yuni a wani shiri kai tsaye domin murnar zagayowar ranar dimokradiyya ta bana.

Ministan yada labarai, Lai Mohammed ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, ranar Alhamis.

Mista Mohammed ya lura da cewa an jera al’amura domin tunawa da ranar kamar laccar jama’a da za a yi a ranar Juma’a 10 ga watan Yuni a masallacin kasa.

A cewar Ministan “Bikin na bana zai kasance karo na hudu da za a yi bikin a ranar 12 ga watan Yuni, bayan bukukuwan da aka yi shekarun  2019, 2020 da 2021.

“A ranar Lahadi, 12 ga Yuni, shugaban kasa zai yi jawabi kai ta kafar yada barai da safe,” in ji shi.

A baya dai ana gudanar da bikin ranar dimokuradiyyar Najeriya a ranar 29 ga watan Mayu kafin shugaba Buhari ya sauya ranar 12 ga watan Yuni domin tunawa da ranar 12 ga watan Yunin 1993, zaben shugaban kasa da gwamnatin mulkin soja ta soke.

A ranar ne aka saba gudanar da hutu aiki a duk fadin kasar amma Mista Mohamed ya ce ma’aikatar kula da harkokin cikin gida ce za ta iya yin irin wannan sanarwar .

Ministan ya kuma ce za a gudanar da adduo’i a masalacin Juma’a da Coci don murnar ranar dimokuradiyyar ta bana.

 

AK/LADAN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *