Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Buhari Ya Taya Dan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar APC Murna

Timothy Choji, Abuja

0 404

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023 murna.

A cikin sakon, shugaban ya ce: “Bayan ya yi nasara, yana da cikakken goyon bayanmu.

“Yanzu dole ne jam’iyyarmu ta hada kai ta goyi bayan takararmu domin samun nasara a zaben 2023 don gwamnatinmu ta ci gaba da tabbatar da tsaron al’ummarmu, bunkasa tattalin arzikinmu da kuma ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa.

“A lokacin zabukan fidda gwani, an samu bangaranci da rashin jituwa a tsakanin ‘yan takarar kuma yanzu da aka kammala  dole ne mu samar da hadin kai a jam’iyyarmu.

“Ta haka ne jam’iyyar APC za ta ci gaba da kasancewa jam’iyyar da za ta fi dacewa da abubuwan da al’ummar Najeriya za su sa a gaba. Yanzu lokaci ya yi da za mu manta  da abin da ya faru a baya.”

 

Jam’iyya Mafi Karbuwa

Shugaban ya lura cewa APC ta kasance mafi karbuwa i ga ‘yan Najeriya.

“Saboda abin da za mu iya yarda da shi shi ne cewa APC ta ci gaba da kasancewa jam’iyyar da za ta fi dacewa da abubuwan da al’ummar Najeriya suka sa a gaba. Amma hanyar da za mu nuna cewa za mu iya ci gaba da wannan aikin ita ce haɗin kai.

“bubuwan da muka kirkiro a 2013 ya wuce tunanin daidaikun mutane. A tare, mun kafa tarihi inda muka zama jam’iyya ta farko a tarihin kasarmu da ta kawar da jam’iyya mai mulki tare da shigar da dan takararmu zuwa Shugaban kasa ta hanyar mika mulki cikin lumana ta hanyar dimokuradiyya.

“Mun yi imani da cewa Bola Ahmed Tinubu zai kiyaye da inganta wannan nasara da kuma abin da aka bari ta dimokradiyya.

“Shi ne dan takarar da ya dace da muradin Najeriya domin shi ne dan takarar jam’iyyar APC kuma a karkashin jam’iyyarmu ta ci gaba da gudanar da ayyukanta,” inji shi.

A cewar shugaban kasar Najeriya na iya samun daukaka da kuma cika makomarta a nahiyar Afirka da ma duniya baki daya.

“Babban abin da ya faru a wannan babban taron jam’iyyarmu shi ne kuzarin ‘yan takarar shugaban kasa kuma daga cikinsu ne muka zabi shugaba mafi farin jini.

“Na aminta kuma na yaba da kishi da amincewa da kai a tsakanin maza da mata na jam’iyyarmu.

“Ina kuma gode wa wakilan da suka yanke shawara mai kyau da ta kai ga fitowar dan takararmu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu,” in ji shugaban.

 

AK/LADAN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *