Rundunar ‘yansandan Najeriya reshen jihar Kano ta bayyana cewa ta tanadi dakarun ‘yansanda 4000 wadanda za su sa idanu don tabbatar da ganin an gudanar da zabukan da ba a kammala cikin kwanciyar hankali da lumana.
Kwamishinan ‘yansanda na jihar ta Kano CP Mamman Dauda shi ya bayyana haka yayin taron masu ruwa da tsaki a ofishin hukumar zaben ta INEC wanda ya mayar da hankali kan zabukan da za a kammala nan gaba a jihar ta Kano.
Mataimakin kwamishinan kan harkokin ayyuka DCP Mu’azu Mohammad da ya wakilci kwamishinan a wajen taron yace rundunar ‘yansanda ta jihar ta Kano da wasu jami’an tsaro sun fitar da tsari wanda zai tabbatar da ganin an gudanar da zabe lami lafiya.
Ya shawarci jam’iyyun siyasar da su gargadi magoya bayansu don su guji bangar siyasa su kaucewa tada hankulan al’umma yayin zaben, kuma duk wanda aka kama da laifin taka doka to shima dokar za ta yi aiki a kansa.
Da yake nasa tsokaci kan batun kwamishina a hukumar zaben ta INEC a Kano Ambasada Abdu Zango yace duk da cewa an yi zaben shugaban kasa da na gwamna lafiya a jihar, an kuma fuskanci tarnaki a zabukan wasu ‘yanmajalisa a matakin jiha da tarayya don haka ne ma za a kammala zabukan da basu kammala ba.
Yace wuraren da abun ya shafa sun hada da Danbatta, Makoda, Dawakin Tofa, Gabasawa,Gezawa, Gaya, Takai, Garko, Wudi, Warawa, Ungogo, Ajingi, Gwarzo, Tudun Wada da Fagge.
Ambasada Zango ya kara jaddada cewa, “hukumar ta INEC za ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da ganin an yi zabe mai nagarta da za a yi wa kowa adalci. Ya ce duk jam’iyyar da ke da korafi ta garzaya kotu don neman hakkinta Kano ta zauna lafiya”.
Wannan taro dai ya samu halartar wakilan jam’iyyun siyasa da kungiyoyin sakai da jami’an tsaro da kafafan yada labarai.
Leave a Reply