Kungiyar malaman kwalejojin ilimi COEASU ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta koma kan teburin tattaunawa da kungiyar domin kammala tattaunawa da ya hada da karin albashi ga ma’aikatan ilimi a kwalejojin ilimi a fadin kasar.
Shugaban COEASU, Dr Smart Olugbeko ne ya yi wannan kiran a Abuja yayin da yake jawabi ga manema labarai kan karin kashi 40% na albashin da gwamnatin tarayya ta yi wa ma’aikatan gwamnati.
Gwamnatin tarayya wajen bayar da wannan kari, ta bayyana cewa, ta yi hakan ne domin baiwa ma’aikatan gwamnati damar dakile illar hauhawar farashin kayayyaki da kuma kara tsadar rayuwa.
Olugbeko ya ce kungiyar ta samu fahimtar juna da tawagar gwamnatin tarayya akan kusan dukkanin batutuwan da aka tabo domin sake tattaunawa sai dai karin albashi wanda kungiyar gwamnati ta ce tana jiran martanin gwamnati.
“A karshe gwamnatin tarayya ta amince da bukatar kungiyar ta hanyar kaddamar da kungiyar FGN/COEASU Renegotiation Team a 2022 karkashin jagorancin Farfesa Kabiru Ishyaku, tsohon babban sakataren hukumar kula da kwalejojin ilimi ta kasa (NCCE).
“An yi kokari daban-daban daga bangaren kungiyar na ganin gwamnati ta sake tattaunawa kan yarjejeniyar 2010 wadda ta baiwa malaman kwalejojin ilimi tsarin albashin da ake biyansu a halin yanzu duk da cewa ya kamata a sake tattaunawa bayan shekaru uku.”
Karin Albashi A Kwalejoji
Sannan ya kara da cewa malamai da sauran ma’aikata a kwalejojin ilimi sun samu karin albashi na karshe a shekarar 2010 wato shekaru 13 da suka gabata.
“Ma’anarsa ita ce, abin da malamai suke samu a shekarar 2010 daidai yake da adadin da suke samu a shekarar 2023.
“Ƙarin albashi ga ma’aikatan ilimi a manyan makarantu ba tallafi ba ne daga gwamnati. A maimakon haka, ya samo asali ne daga tattaunawa tsakanin gwamnati da kungiyoyin saboda ficewar tsarin ta fuskar kayyade aikin da ke jawo alawus-alawus daban-daban ga ’yan kwadago daban-daban,” Dr Olugbeko ya kara da cewa.
Sai dai COEASU ta nuna rashin jin dadin ta game da matakin karin albashin da ya ware wasu nau’ikan ma’aikata da suka hada da malamai da sauran ma’aikata a manyan makarantun.
Shugaban kungiyar ta COEASU ya kara da cewa, “Kungiyar ta yi matukar kaduwa da matakin da gwamnati ta dauka na kebe wasu nau’o’in ma’aikata da suka hada da malamai da sauran ma’aikata a manyan makarantu duk da cewa kungiyoyin daban-daban na wannan fanni sun yi wa gwamnati tuhume-tuhume kan karin albashi.”
Leave a Reply