Take a fresh look at your lifestyle.

Gwadabe ya rasu a lokacin da aka fi bukatarsa…. Abba Kabir Yusuf

Yusuf Bala Nayaya,Kano.

0 153

Zababben gwamnan jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya Injiniya Abba Kabir Yusuf ya mika sakon ta’aziyarsa ga iyalai da al’ummar jihar Kano kan rasuwar Alhaji Musa Gwadabe gogaggen dan siyasa kana tsohon ministan kwadago kuma tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano Alhaji Musa Gwadabe.

 

Abba Kabir Yusuf ya bayyana marigayin a matasin gwarzo abin koyi da rasuwarsa ta zo a lokacin da aka fi bukatarsa a matsayinsa na jagora da zai wahala a maye gurbinsa.

 

Zababen gwamnan jihar na Kano Abba Kabir Yusuf wanda a cikin wasikar da sakataren yada labaransa Sunusi Bature Dawakin Tofa ya rattabawa hannu ya kalubalanci ‘yansiyasa na wannan zamani su yi aiki tukuru wajen ganin sun samar da ayyuka nagari ga al’umma da ba za a mance da su ba kamar yadda aka gani a rayuwar marigayin.

 

Abba Kabir Yusuf yayi addu’ar Allah Ya jikan marigayin ya sanya Jannatul Firdaus ta zamo makoma a gare shi.

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *