Najeriya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da kungiyar kasashen Afirka, Caribbean da Pacific, OACPS.
Yarjejeniyar MoU wacce aka rattaba hannu a kai a Abuja, Najeriya, na kafa tsarin tattaunawa kan hadin gwiwar fasaha tsakanin sakatariyar kungiyar kasashen Afirka, Caribbean da Pacific (OACPS) da gwamnatin Najeriya.
Ministan harkokin wajen kasar Geoffrey Onyeama da babban sakataren kungiyar ta OACPS, Georges Rebelo Pinto Chikoti ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a madadin Najeriya.
Mista Onyeama wanda ya yaba da kyakkyawan matakin hadin gwiwa tsakanin Najeriya da OACPS ya bayyana cewa makasudin sanya hannu kan yarjejeniyar ita ce karfafa wannan alaka.
Ministan ya kuma bayyana jin dadin Najeriya ga kungiyar OACPS ba kawai don rattaba hannu kan yarjejeniyar ba da tsarin da ya ce yana da karfi sosai har ma da kafa Sakatariyar OACPS a cikin kasar.
Ya kuma bayyana cewa Najeriya za ta nemo tsarin da zai karfafa wannan alakar, yana kuma fatan siyasa za ta inganta ta.
Mista Onyeama ya yi alkawarin daukar matakin gaggawa na samar da hanyoyin karbar bakuncin Sakatariyar a Najeriya.
Sakatare Janar na Kungiyar Kasashen Afirka, Caribbean da Pacific (OACPS), Georges Rebelo Pinto Chikoti ya bayyana cewa sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da OACPS alama ce ta sha’awar Najeriya da kuma sadaukar da kai ga hadin gwiwar Kudu-maso-Kudu.
Ya kuma nuna farin cikinsa da yadda Najeriya ta amince da karbar bakuncin Sakatariyar.
A cewar Chikoti, OACPS za ta ci gaba da fata da kuma dogaro da goyon bayan Najeriya wajen karfafa wannan alaka.
Mista Chikoti ya kuma bayyana cewa, rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da kuma taron karawa juna sani da ake gudanarwa a Najeriya na daga cikin matakan da ake dauka na bunkasa hadin gwiwar yankin kudu maso kudu da ke nuna kwarin gwiwa na kasashe mambobin kungiyar kan wannan alaka.
Ya ci gaba da cewa, rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Najeriya da OACPS, wani tabbaci ne na irin daukakar da Najeriya ke wakilta ba ga Afirka kadai ba har ma da sauran kasashen duniya.
Leave a Reply