Gwamnatin jihar Katsina ta kulla yarjejeniyar Bunkasa kyakkyawan yanayin kasuwanci a jihar
Kamilu Lawal,Katsina.
Gwamnatin jihar Katsina ta rattaba hannu akan wata yarjejeniyar fahimtar juna tsakaninta da wasu kanfanoni domin samar da cikakkiyar dama wajen kafawa da gudanar da kasuwanci a tsakanin abokar hudda a jihar da kasa baki daya
Kanfanonin da gwamnatin jihar ta kulla yarjejeniyar da su sun hada da Afri Nigeria Limited da ATM Power Limited da kuma Asbat Construction Limited
Wakilin kamfanonin a wajen yarjeniyar Tope Banjoko ne ya sanya hannu a madadin kanfanonin yayin da shugaban hukumar bunkasa saka jari ta jihar Katsina Ibrahim Tukur Jikamshi ya sanya hannu a madadin gwamnatin jihar Katsina
Idan yarjejeniyar ta soma aiki ana sa ran kamfanonin zasu samar da ingantaccen yanayin gudanar da kasuwanci ga al’ummar jihar ta hanyar samar da wadatattar wutar lantarki da dakunan kwana da asibitoci da makarantu da matsugunnan cibiyoyi hadi da dukkanin wasu abubuwan da saka jari da bunkasa kasuwanci ke bukata a wani kebataccen wuri da gwamnatin jihar ta samar domin bada dama ga masu sha’awar saka na ciki da wajen najeriya da ake kira da Economic Zone a turance
Shugaban hukumar bunkasa saka jarin ta jihar Katsina Ibrahim Tukur Jikamshi ya bayyana cewa samar da kebattaccen wurin a jihar Katsina ya biyo bayan kaddamar da wani shiri da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi na samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci a najeriya kalkashin hukumar tattalin arzikin kasa wato NEC kalkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da mataimakan gwamnonin jihohin najeriya da nufin samarwa najeriya yanayi mai kyau ga masu juba jari daga ciki da wajen kasar domin bunkasar tattalin arziki
“Ibrahim Jikamshi yace;” Muna gina wani kebantaccen wuri da ake kira Economic Zone wanda kamar yadda tsarin yake ana saka mashi dukkanin wani abu da kanfani zai bukata kamar Wuta da Ruwa da gidajen kwana da makarantu da duk wani abu da kasuwanci ke bukata domin cigaba”.
“Wannan zama da muke a yanzu ya faru ne bisa yadda muka sanar da duniya abinda muke yi da kuma damar da muka bayar ga masu saka jari a fadin duniya na suzo ga dama ta samu a jihar Katsina domin bada gudummuwa ga saka jari da cigaban kasuwanci”.
Shima a nasa jawabin, wakilin kanfanonin da aka kulla yarjejeniyar dasu, Tope Banjoko ya bayyana cewa daga cikin ababen da yarjejeniyar zata samar akwai gine gine da wadataccen hasken wutar lantarki ga abokan hulda domin inganta kasuwanci da bunkasa saka jari domin bunkasa harkokin tattalin arziki ga jihar da al’umma baki daya
Leave a Reply