Tantacewa tsakanin kwamitin karbar mulki da wanda zai ba da mulki ta ci tura a Kano Arewa maso Yammacin Najeriya, bayan da kwamitin karbar mulkin jam’iyyar NNPP karkashin jagorancin Dakta Baffa Abdullahi Bichi ke ci gaba da fuskantar turjiya daga bangaren kwamiti na jam’iyyar APC mai mulkin Kano karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
A cewar shugaban kwamitin karbar mulkin na NNPP Dakta Bichi Duk sanda kwamitinsu ya nemi hada kai da bangaren masu mulki suna fuskantar tasgaro in da bangaren na APC ke da’awar cewa kwamitinsu ba zai aiki ba sai Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya rantsar da shi, lamarin da ya gagara sama da makonni hudu, abin da kuma bangaren na NNPP ke ganin akwai wata jikakkiya.
Dakta Bichi ya kara da cewa bangaren gwamnatin APC baya yin abin da ya dace kasancewar ba wannan ne karon farko ba da a Kano wata gwamnatin jam’iyya ke mika mulki ga wata inda ya ba da misalai da dama ciki kuwa har da yadda Malam Ibrahim Shekarau na APP ya karbi mulki a hannun Dakta Rabiu Musa Kwankwaso na PDP a 2003, wadanda dukkansu na da jam’iyyunsu kuma manufofinsu sun banbanta.
Bichi ya kara da cewa “Mun fahimci cewa ita bangaren gwamnati so suke ayi kwamiti daya inda suka nemi mu ba da mambobi uku, ma’ana a karshe za a samar da kwamiti da za su kasance suna da kaso tamanin cikin dari nasu mu kuma muna da kaso ashirin cikin dari. Abin duba shine ba jam’iyyarmu daya ba, ba akidarmu daya ba, ba manufarmu daya ba. Ta yaya za mu hadu a kwamiti daya na karbar mulki? Da alama bangaren gwamnati bai fahimci abin da ake son yi ba. Aikin mai karbar mulki daban, aikin mai ba da mulki daban.”
A cewar Bichi dai shirye-shiryen karbar mulkinsu yayi nisa cikin hikima da tsari da kwanciyar hankali,kuma idansu a bude don shine aikin da Injiniya Abba Kabir Yusuf zababben gwamnan ya ba su don sanin halin da gwamnati take a yanzu da inda za ta nan gaba.
Har ila yau shugaban kwamitin ya kara da cewa a mako mai zuwa kuma za su fara ganawa da manyan sakatarori na ma’aikatun gwamnati a otel din Tahir Guest Palace, na biyu sai ganawa da manyan shugabanni na ma’aikatun gwamnati da kananan kwamitoci za su zauna da su a lokaci da za a bayyana nan gaba, na uku kuma za su gana da shugabannin maaikata da ake kira DPM na kananan hukumomi 44 na jihar Kano.
Fatan jam’iyyar NNPP dai shine karbar mulki cikin nasara ta yadda Injiniya Abba Kabir Yusuf zai jagoranci jihar da aiwatar da shirye-shirye managarta da jam’iyyar NNPP ta tsaro don ciyar da jihar ta Kano gaba a cewar Dakta Bichi shugaban kwamitin na karbar mulki.
Leave a Reply