Matasan Atlas Lions na Morocco a daren Lahadi sun doke Amajimbos ta Afirka ta Kudu da ci 2-0 a wasa na biyu na rukunin B da suka fafata a zagayen farko na rukunin B inda Najeriya ke kan gaba a teburin rukunin.
KU KARANTA KUMA: U17 AFCON: Ugbade ya kira ‘yan wasa 48 zuwa sansani
Duk da cewa an tashi babu ci, Kyaftin na Morocco, Abdelhamid Boudlal da Adam Hanin ne suka zura kwallo a ragar Morocco a karawar ta biyu.
Nasarar da aka yi da ci 2-0, ya sa Morocco ta zama ta daya a teburin rukunin B, idan an tuna, a halin yanzu Golden Eaglets ce ta biyu bayan ta samu nasara a kan Zambia da ci 1-0 a wasannin farko.
Najeriya za ta kara da Morocco ranar Laraba, yayin da Afirka ta Kudu da Zambia za su kara da juna. A ranar 3 ga watan Mayu ne za a yi wasa tsakanin Najeriya da Morocco da karfe 7 na dare agogon Najeriya.
Rukunin B
Najeriya da Morocco – 3 ga Mayu, Laraba, 7 na yamma agogon Najeriya
Zambia da Afirka ta Kudu – 3 ga Mayu, Laraba, 10 na dare agogon Najeriya
Leave a Reply