Gwamnan jihar Osun kuma dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Adegboyega Oyetola ya yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu, ya kuma bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da gudanar da sana’o’insu ba tare da wata tsangwama ba. Gwamnan ya yi wannan kiran ne a wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa Ismail Omipidan ya fitar a ranar Lahadi. Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su tabbatar da bin doka da oda. Don haka ya umurci jami’an tsaro da su dauki kwararan matakai domin hana tabarbarewar doka da oda.
KU KARANTA KUMA: Sanata Adeleke ya lashe zaben gwamnan jihar Osun.
Da yake magana kan zaben da aka kammala kwanan nan, Omipidan ya bayyana cewa Gwamnan Osun ya amince da sakamakon zaben gwamna a jihar kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar a ranar Lahadi. Sai dai ya bayyana cewa jam’iyyar za ta mayar da martani yadda ya kamata bayan nazarin sakamakon da kuma tuntubar masu ruwa da tsaki a jam’iyyar. Idan dai ba a manta ba Sanata Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya doke gwamna mai ci Adeboyega Oyetola a zaben da aka kammala a ranar Asabar. Jami’in zaben Farfesa Oluwatoyin Ogundipe wanda shi ne mataimakin shugaban jami’ar Legas a ranar Lahadi ya dawo da Adeleke, bayan da ya samu adadin kuri’un da ake bukata da kuma cika wasu dokoki.
Leave a Reply