A ranar Talata ne gwamnatin jihar Bauchi ta fara sayar da takin zamani na noman shekarar 2023 kan farashin Naira 15,000 kan kowane buhu.
Gwamna Bala Mohammed ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da kakar noma da sayar da taki na shekarar 2023 a garin Azare, hedikwatar karamar hukumar Katagum ta jihar.
Ya ce, “An yi hakan ne domin a karfafa wa manoma gwiwa don samun girbi mai yawa a wannan damina.
“An kashe makudan kudade wajen siyan tireloli sama da 200 na takin NPK, sinadarai don magance kwari da kuma rigakafin dabbobi.”
Gwamnan ya umurci ma’aikatar noma ta jihar da ta sanya ido kan duk wani mummunan hali na tallace-tallace da rarraba takin da kayan masarufi.
Mohammed, wanda ya nuna damuwarsa kan yadda manoman ke kasa samun dabarun da ake bukata domin inganta ayyukansu, ya ce an yi kokarin daukar karin ma’aikatan da za su magance kalubalen.
A nasa jawabin, kwamishinan noma Jidauna Mbami ya bukaci manoma da su dasa iri da wuri, duba da hasashen da hukumar kula da yanayi ta Najeriya NIMET ta yi, inda ta yi hasashen samun karancin ruwan sama a yankin arewa maso gabashin kasar.
Shima da yake nasa jawabi shugaban kungiyar manoma ta Najeriya AFAN a jihar, Alhaji Yusuf Gambo ya yabawa gwamnatin jihar bisa tallafin kudin taki da kayan masarufi.
“Wannan karimcin zai taimaka matuka wajen karfafa noma mai girma a jiharmu mai albarka a wannan damina,” in ji shi.
KU KARANTA KUMA: Masu ruwa da tsaki sun saka takin zamani a Najeriya
Leave a Reply