Gwamnan jihar Neja arewa ta tsakiyar Najeriya Abubakar Sani Bello ya buƙaci rudunar ‘yan sandan Najeriya ta, ƙara tura ƙarin jami’anta na kwantar da tarzoma (Mobile Police) zuwa yankunan da ke fama da matsalar tsaro domin daƙile zirga zirgar da ‘yan bindiga ke yi daga makwabtan jahohi zuwa jihar Neja.
Gwamnan ya buƙaci hakan ne a lokacin da mataimakin sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya mai kula da shiya ta 7 Aliyu Garba ya ziyarce shi a gidan gwamnati da ke Minna.
Gwamna Sani Bello ya ce jihar Neja baya ga matsalar tayar da zaune tsaye daga ɓangaren matasa tana cikin jihohin ƙasar da aka sansu da zaman lafiya da kwanciyar hankali kafin ɓullowar ayyukan ‘yan bindiga.
Gwamnan ya ƙara da cewa a ɓangaren matasa tuni gwamnati ta bayar da umurnin kawo ƙarshen ayyukansu a dukkanin faɗin jahar Neja.
Har ila yau Abubakar Sani Bello ya ce ana samun ƙaruwar ayyukan ‘yan bindiga a wasu sassan jahar Wanda Kuma hakan na damun gwamnati matuka.
A don haka gwamnan ya bukaci sabon matakamkin sifeta janar din yan sandan mai kula da shiya ta 7 da Kuma alummar jahar da su himmatu wajan ganin an kawo karshen matsalar.
A jawabinsa tun da farko mataimakin sifeta janar ɗin Aliyu Garba ya bayyana cewa ya kawo ziyarar ne domin sanin irin halin da ake ciki ta yadda rudunar yan sandan Najeriya don haɗa hannu da sauran jami’an tsaro da nufin kawo ƙarshen matsalar tsaro a jahar Neja da ma ƙasa baki ɗaya.
Aliyu Garba ya ƙara da cewa abu mafi mahimmanci daga ɓangaren gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki shine na ganin an Samar da dukkanin abunda suka kamata a yakin da ake Yi da yan ta’adda domin ceto yan jihar da ma ƙasa daga halin da suka tsinci kansu.
Mataimakin gwamnan jihar Ahmad Muhammed Ketso da zaɓaɓɓen gwamna Umar Muhammed Bago da mataimakin sa Yakubu Garba sun kasance a wurin yayin da Aliyu Garba ya sami rakiyar kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja CP Ogundele Ayodeji da sauran manyan jami’an rudunar ‘yan sanda.
Leave a Reply