Shugabancin Majalisa: kungiyar Hadaddiyar Masu Ruwa da TSaki A APC sun nemi mukamin mataimakin shugaban majalisa
Nura Muhammed,Minna.
Kungiyar dake fafutukar kare muradin jamiyar APC a jahar Neja ta bukaci kwamitin gudanarwa jamiyar na kasa da ya sauya matakin da ya dauka na amincewa da Kuma nuna goyon baya ga wasu mambobin majalisar a matsayin shugabanta daga yankin kudu maso kudancin kasar da Kuma mataimakin sa daga arewa maso yammacin Najeriya domin dai daita sahun mukaman a mulkin demokradiya da ake ciki ta hanyar yin gaskiya a lamuran.
Kungiyar ta bakin Shuaib Awaisu Kuta jami’in shirya gamgamin nuna bacin rai kan matakin da jamiyar ta dauka, shine ya bayana matsayin su a kungiyance a taron manema labarai da suka kira a garin Minna inda suka ce dole sai kwamitin tare da sabon zabebben shugaban kasa Bola Ahamad Tunubu sun duba yadda kowane bangare a kasar zai sami rabo na mukami a majalisun taraya kasar kamar yadda yake a tsarin jamiyar APC na yin adalci da samar da hadin Kai.
A cewar Awaisu Kuta jahar Neja ta kasance kan gaba a kuri’un da suka kaiga Samar da nasara a zaben da ya gudana inda aka sami sanatoci 2 da yan majalisar wakilai 7 da Kuma yan majalisar dokoki 21 cikin 27 da ake da su a jahar Neja.
Awaisu Kuta ya Kara da cewar duba ga irin yadda jihar ta bada gudumuwa, akwai bukatar ganin an saka mata da mukamai da yan jahar zasu yi alfahari musamman a majalisa domin kara basu kwarin gwiwar cigaba da bautawa jamiyar a dukkanin harkokin da suka shafe ta.
Kungiya ta Kuma bukaci dukkanin masu ruwa da tsaki da su duba lamarin domin kawo maslaha a fadi tashin da ake yi na ganin jamiyar ta APC ta cigaba da karbuwa a zukatan yan kasar.
Sun Kuma nuna damuwar su ga yadda ake son nunawa yankin arewa ta tsakiyar kasar wariya duk da irin gudumuwar da suka bada a babban zaben da ya gabata.
Har Ila yau jagoran gamgamin ya shawarci kwamitin da Kuma sabon shugaban kasa da su duba irin gudumuwar da sanata Mai wakiltan arewacin jahar Neja Sanatan Sani Musa 313 ya bada a majalisa na kawo cigaba a Najeriya ta hanyar saka masa da mukamin mataimakin shugaban majalisar dattijai, wanda a cewar su ta haka ne yankin zai san ana damawa da shi.
Awaisu Kuta ya ce ” Sanata Sani Musa 313 ya cancanci a saka masa da mukami a majalisa bisa irin yadda ya bada gudumuwar a majalisar da Kuma yadda ya kashe kundin sa duk don ganin jamiyar APC ta sami nasara a zaben da ya gudana.”
kungiyar ta bukaci jamiyar APC da ta martaba tsarin da ya kafa ta na adalci da zaman lafiya da hadin Kai, tunda mukamin shugaban majalisa ta mika shi ga yankin kudu maso kudanci ya kamata a mika mataimakin shugabancin majalisar zuwa ga yankin arewa ta tsakiyar kasar musamman a jahar Neja.
Leave a Reply