Take a fresh look at your lifestyle.

Zelenskiy Ya Ce Har yanzu Ba a Fara Luguden Wuta da ake jira ba

0 110

Shugaba Volodymyr Zelenskiy ya ce har yanzu ba a fara kai farmakin da aka dade ana jira a Ukraine ba kan sojojin da ke mamaye da Rasha, duk da cewa janar-janar dinsa ya yi ikirarin samun nasara a fagen daga cikin watanni.

 

 

Kyiv ta ce ta fatattaki sojojin Rasha a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata a kusa da gabashin birnin Bakhmut a hare-haren cikin gida, yayin da ake ci gaba da shirin kai wani dauki ba dadi da ya kunshi dubun-dubatar sojoji da daruruwan tankunan kasashen yamma.

 

 

“Har yanzu muna buƙatar ƙarin lokaci,” in ji Zelenskiy a cikin wata hira da masu watsa shirye-shiryen Turai.

 

Zelenskiy ya ce sojojin Ukraine “sun riga sun karbi isassun kayan aiki daga abokan kawancen kasashen Yamma don yakinsu amma suna jiran cikkaken motoci masu sulke” su isa domin rage musu asarar da suke yi.

 

 

A wani babban mataki na goyon bayan soji na yammacin Turai ga Ukraine, Birtaniyya ta sanar da aikewa da makami mai linzami na Storm Shadow da za su baiwa Kyiv damar kai hari a cikin zurfin layin Rasha.

 

 

“Makullin anan shine baiwa Ukraine wannan damar. Don kare kanta,” Sakataren Tsaro Ben Wallace ya fada wa majalisar dokoki a London.

 

 

Kasashen yammacin duniya, ciki har da Amurka, a baya sun ja baya daga samar da makamai masu cin dogon zango saboda tsoron tada hankalin Rasha ‘ramuwar gayya.’ Wallace ya ce Birtaniya ta auna hadarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *