Jakadan Amurka a Afirka ta Kudu ya zargi kasar da bai wa Rasha makamai da alburusai don yakin da ta ke yi a Ukraine ta hanyar jirgin ruwan dakon kaya da ya tsaya a asirce a wani sansanin sojin ruwa da ke kusa da birnin Cape Town na tsawon kwanaki uku a watan Disamba.
An gabatar da tambayoyi a majalisar dokokin Afirka ta Kudu kuma shugaba Cyril Ramaphosa ya ce ana gudanar da bincike.
Ambasada Reuben Brigety ya ce Amurka na da tabbacin an loda kayan ne a kan jirgin ruwan Rasha a sansanin sojin ruwa na Simon’s Town sannan aka kai shi Rasha, a cewar rahotannin nasa da wasu kafafen yada labarai na Afirka ta Kudu suka fitar.
Ramaphosa ya kasance a Cape Town yana amsa tambayoyi a Majalisar lokacin da labarin kalaman Brigety ya bazu.
Da wani dan majalisa ya tambaye shi game da makaman da alburusai, shugaban ya amsa da cewa “ana duba lamarin, kuma nan gaba kadan za mu iya yin magana a kai.”
Ramaphosa dai ya ki yin karin bayani, inda ya ce akwai bukatar a gudanar da bincike.
Shugaban ‘yan adawar siyasa, John Steenhuisen, ya tambayi shugaban kasar ko Afirka ta Kudu tana “ba da makamai ga sojojin Rasha da ke kashewa da kuma nakasa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba?”
Steenhuisen ya kuma tambaya ko Ramaphosa zai iya tabbatar da cewa “makamin yaki” an ɗora wa jirgin ruwan Rasha.
Kayayyakin harsasai sun zama matsala ga Rasha a yakin. Shugaban sojojin Rasha masu zaman kansu Wagner ya koka a makon da ya gabata cewa sojojin hayarsa a Ukraine suna fuskantar matsananciyar karancin abinci.
A cikin wata sanarwa da aka fitar daga baya a ranar Alhamis, ofishin Ramaphosa ya amince da wani jirgin ruwa na Rasha mai suna Lady R ya tsaya a Afirka ta Kudu, amma ofishin bai bayyana inda ko kuma manufar tsayawarsa ba.
Sanarwar ta soki jakadan na Amurka da ya fito fili ya kuma ce akwai yarjejeniya cewa jami’an leken asirin Amurka za su bayar da duk wata shaida da suke da ita don taimakawa Afirka ta Kudu binciken.
A shekarar da ta gabata ne Amurka ta kakaba wa Lady R da wani kamfani na Rasha da ke da alaka da shi, wato Transmorflot LLC, takunkumi bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine saboda shigar da kayan yaki da makamai.
Brigety ya fada a ranar alhamis din da ta gabata cewa zargin da kasar Afirka ta Kudu ta yi wa kasar Rasha a lokacin da ta mamaye kasar Ukraine abu ne mai matukar muhimmanci kuma ya sanya ayar tambaya kan matakin da Afirka ta Kudun ta dauka na tsaka mai wuya.
Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press ya tabbatar da kansa cewa Lady R ta tsaya a sansanin sojojin ruwa na garin Simon a lokacin da Brigety ya ambata.
Leave a Reply