Take a fresh look at your lifestyle.

Jahar Kebbi Da Masar Sun Hada Kai Kan Aikin Noma

0 382

Gwamnatin jihar Kebbi ta ce za ta hada gwiwa da kwararrun masana harkokin noma da kiwo na kasar Masar domin ci gaban jihar.

 

Gwamna Atiku Bagudu ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar kwararrun masana harkar noma daga Masar da suka ziyarce shi a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi, a ranar Juma’a.

 

Ya ce gwamnatinsa ta yi imani da hadin gwiwa da hadin kai a matsayin muhimman abubuwan ci gaban jihar.

 

‘Jihar na da albarkar noma da yawa kuma an yi mata kima a matsayin jiha ta biyu mafi yawan kiwon dabbobi a kasar nan.

 

“Bugu da kari, jihar ta zama hanyar shiga yammacin Afirka wajen kiwon dabbobi saboda dabarun da take da shi na raba iyaka da jamhuriyar Nijar da jamhuriyar Benin.

 

“Tuni mun sanya hannu kan wata yarjejeniya ta bangarori uku da Kwanni a Jamhuriyar Nijar da kuma Maleville a Jamhuriyar Benin kan bunkasa kiwon dabbobi,” in ji Gwamnan.

 

Bagudu ya kuma bayyana al’ummar jihar a matsayin masu aiki tukuru kuma a shirye suke su tsara hanyoyin zamani kan noma da kiwo.

 

Ya kuma yabawa shugaban kungiyar manoma shinkafa ta kasa RIFAN, Alhaji Aminu Goronyo bisa yadda suka gudanar da ziyarar da kuma shirye shiryen hadin gwiwa a fannin noma.

 

“Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ya yi alkawarin ci gaba a kan nasarorin da aka samu kan farfado da aikin gona domin samar da abinci da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar a matakin kasa.

 

“Har ila yau, a nan jihar, zababben gwamnan jihar, Dakta Nasir Idris, ya tabbatar da irin wannan kudiri na karfafa juyin juya halin noma da gwamnati mai ci a matakin jiha ta fara.”

 

Tun da farko shugaban RIFAN, Alhaji Aminu Goronyo, ya shaida wa gwamnan cewa kwararrun ‘yan kasar Masar karkashin jagorancin Walid Soliman-Morsy sun je jihar ne domin hadin gwiwa kan bunkasa noma.

 

Ya bayyana cewa kwararrun a shirye suke don bunkasa kadada da dama na filin Fadama a jihar ta hanyar horar da manoma, amfani da hanyoyin noman zamani, fasaha da kwarewa.

 

Goronyo ya ce tawagar za ta kuma ziyarci jihohin Legas da Ogun da kuma Calabar da ke Kuros Riba domin gudanar da irin wadannan ayyukan.

 

Maaikatan gona na Masar, karkashin jagorancin Mista Soliman-Morsy, sun bayyana cewa sun je jihar ne domin hadin gwiwa da gwamnati domin lalubo wuraren da ake da sha’awar noma da kiwo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *