Majalisar dattawan Najeriya a ranar Talata, ta dakatar da zamanta kan mutuwar dan majalisa mai wakiltar mazabar Egor/Ikpoba-Okha a jihar Edo, Mista Jude Idehen. Mista Idehen, har zuwa rasuwarsa, dan majalisar wakilai ne a karkashin babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya, PDP. Majalisar dattijai bayan da ta dawo daga hutun makonni biyu, ta dage zamanta zuwa ranar Laraba 20 ga watan Yuli domin karrama marigayin wanda ya rasu a ranar 1 ga watan Yuli yana da shekaru 52 a duniya. Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ajayi Boroffice ne ya gabatar da kudurin dage zaman majalisar, sannan kuma shugaban marasa rinjaye, Sanata Philip Aduda ya goyi bayansa. Majalisar ta kuma yi shiru na minti daya domin alhinin marigayin kafin ta dakatar da zaman ranar Talata wanda mataimakin shugaban majalisar, Ovie Omo-Agege ya jagoranta.
Leave a Reply