Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnan Jihar Kwara Ya Nada Etsu Patigi A Matsayin Amirul-Hajj Na 2023

0 132

Gwamnan Jihar Kwara, Alhaji AbdulRahman AbdulRazaq ya amince da nadin Etsu Patigi, Alhaji Umar Bologi II, a matsayin Amirul-Hajj na aikin Hajji na shekarar 2023 a kasar Saudiyya.

Amirul Hajj din ya kuma kira Shugaban Tawaga zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana shine don tallafawa hukumar jin dadin Alhazai ta jiha a kokarinta na ganin zaman Alhazai a kasa mai tsarki.

Amirul Hajj zai kuma baiwa alhazai tallafin ruhi don gudanar da ayyukan hajji.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Jimoh Jumoke ya fitar.

Sarkin kuma shine mataimakin shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta jiha.

A halin da ake ciki, Hukumar karkashin Shugabancin Dakta Abdulkadir Sambaki da Sakataren Zartaswa, Alhaji Abdulsalam Abdulkadir sun yi maraba da nadin mai martaba Sarkin a daidai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiryen aikin Hajjin 2023 gabanin kaddamar da jirgin da za a sanar nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *