Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnonin Arewa ta Tsakiya Sun Musanta Cewa Sun Yi Tsokaci Kan Zoning Ta NASS

0 193

Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya ce Gwamnonin Arewa ta Tsakiya ba su yi wata sanarwa a bainar jama’a ba kan tsarin shiyya-shiyya na mukaman majalisa.

Gwamnan ya musanta wani rahoto da kafafen yada labarai suka yada cewa sun ki amincewa da matsayin shugabannin jam’iyyar kan lamarin.

AbdulRazaq ya ce Gwamnonin a matsayinsu na shugabannin jam’iyyar da suka fito daga yankin, ba za su iya daukar matakin adawa da matsayar jam’iyyar ba, sai dai suna gudanar da tarurrukan dabaru da masu ruwa da tsaki daban-daban don samar da kyakkyawar manufa ga yankin Arewa ta Tsakiya.

“Kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa mun ki amincewa da matsayin jam’iyyar don haka wani bangare ne na tsarinmu. Ba gaskiya ba ne. Muna da hanyoyin sadarwar mu, kuma abin da muke bincike ke nan,” in ji Gwamnan a wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Rafiu Ajakaye ya fitar.

Sanarwar ta kara da cewa Gwamnonin Arewa ta Tsakiya ‘yan jam’iyya ne kuma ba za su yi wata magana ko yin wani abu da zai zubar da shugabancinta ba ko kuma haifar da tashin hankali da za a iya kaucewa a cikin harkokin siyasa inda suka jaddada cewa, ba haka suke ba.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *