Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Abuja daga birnin Landan, inda ya kwashe kwanaki 13 yana jinya.
Shugaba Buhari wanda ya dawo a yammacin ranar Talata, ya samu tarba daga shugaban ma’aikatan fadar sa, Farfesa Ibrahim Gambari da kuma ministan babban birnin tarayya, Mohammed Bello.
Shugaba Buhari ya tafi kasar Birtaniya ne a ranar 3 ga watan Mayu domin bikin nadin sarautar Sarki Charles III, wanda ya gudana a ranar Asabar 6 ga watan Mayu.
Bayan haka, ya tsawaita zamansa na tsawon mako guda, domin girmama ganawa da likitan hakori.
Ana sa ran shugaban kasar zai jagoranci zaman majalisar zartarwa ta tarayya gobe Laraba.
Leave a Reply