Census: Hukumar kidaya ta kasa a Jihar Neja ta bada tabbacin gudanar da kidaya da zai Sami karbuwa ga alumma.
Nura Muhammed,Minna.
Kwamishinan kula da jahar Neja arewa ta tsakiyar Najeriya a hukumar kidaya ta kasa NPC Muhammad Dattijo Usman ya bada tabbacin hukumar na gudanar da sahihin kidayar jama’a da gidaje da zai kasance karbabe a dukkanin fadin kasar.
Muhammad Dattijo Usman ya bayana haka ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a cibiyar kungiyar yan jaridu na IBB pen house dake Minna fadar gwamnatin jahar Neja.
Kwamishinan ya ce bayanan dake kunshe cikin jawaban da aka tsara na tambayoyi a takardun da hukumar zata Yi anfani da su Basu dauke da bayani kan addini ko yare ba ila cikakkun bayanai kan yankunan da batun tattalin arzikin alumma.
Dattijo Usman ya Kara da cewar babban aikin da hukumar ta Sanya a gaba shine na Samar da bayanai kan yawan yan Najeriya daga lokaci zuwa lokaci.
Kwamishinanan ya Kara da cewar hukumar a shirye take ta gudanar da kidayar da zai kasance na zamani Wanda ke zama irin sa na farko a tarihin kasar.
Har ila yau kwamishinanan ya ce hukumar ta gudanar da manyan ayyukan 33 inda ya rage biyu Wanda shine batun gwajin sabon naurar PDA’s da Kuma Kara gwajin na’urorin da aka gwada su a bayan.
Dattijo Usman ya ce dage aikin kidayar bashi da nasaba da Rashin kudin kamar yadda ake ta alakanta hakan, inda ya ce yanzun haka hukumar na jiran umurni ne domin kaddamar da aikin na kidayar alumma da gidaje.
Nura Muhammed,Minna.
Leave a Reply