Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sake nada Dr. Mahmuda Isah a matsayin kwamishinan zabe a hedikwatar INEC dake Abuja a karo na biyu kuma na karshe.
Isah, wanda ke da digirin digirgir a fannin shari’ar Man Fetur, ya yi rantsuwar kama aiki ne a yayin taron mako-mako na Hukumar, wanda ya samu halartar Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, kwamishinonin hukumar na kasa da kuma sakataren hukumar.
Farfesa Yakubu yayi kira da ya kasance mai biyayya ga al’ummar Najeriya da kuma bin tanade-tanaden doka a koyaushe.
An fara nada Isah ne a watan Janairu, 2018. Ya yi aiki a jihohin Jigawa da Kaduna kafin wa’adinsa na farko ya kare a watan Janairu, 2023. An tura shi babban birnin tarayya.
Leave a Reply