Yayin da ake tunkarar yanayi na damina masana da masu ruwa da tsaki kan harkar muhalli na kira ga al’ummar jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya da su tashi haikan wajen yashe magudanan ruwa don kaucewa ambaliyar ruwa.
A shekarar da ta gabata dai a jihar ta Kano kamar wasu jihohi makota irin na Jigawa sun ga yanayi na ambaliyar ruwan sama kamar a kasuwannin Kurmi da kasuwar Kantin Kwari baya ga wasu sassa na jihar inda aka yi asarar dumbin dukiyoyi wasu lokutan ma har da asarar rayuka.
Duba da fargabar da aka gani a bara tuni masana suka fara jan hankalin al’umma kan su dauki matakai na kaucewa ambaliyar ruwa musamman duba da yanayi na zafi da ake ciki, wanda masana yanayi ke hassahen cewa haka kuma za a tsammaci ruwan sama mai yawa a wannan shekara da muke ciki, don haka kwararrun ke ganin ya zama wajibi al’umma su dauki matakai na kandagarki musamman batu na yashe magudanan ruwa.
Kwamared Saleh Aliyu Jili shine shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Kano SEMA ya ba da shawarwari ga al’ummar jihar ta Kano don kaucewa amabaliyar: ”Kiran mu ga mutanen Kano gaba daya shine kowa ya tabbatar ya yashe magudanan ruwa tun daga matakin gida, a gidanka ka san inda ruwa ke kwanciya in cikewa ne a cike in kuma yashewa ne a yashe. Idan a cikin birni ne ka tabbatar kwatar da ke biyowa daga cikin gidanka a gyare take ko a share take, har a kai zuwa unguwa zuwa matakin babbar kwata inda gwamnati za ta yi aikin yashewa, koda kuwa gwamnatin bata yi ba, jama’a su hada kai kada a jira gwamnatin a yashe magudanan. Gayra kayanka bai zama sauke mu raba.. Ka tsare lafiyarka da ta iyalanka.”
Wani abu da mutane kan yi sakaci da shi shine rashin ba da kulawar da ta dace idan an ga hadowar hadari ko iska a lokacin na damuna, kan wannan ma Kwamared Jili ya ja hanhalin al’umma akai: “A dangane da tsawa idan mutane sun ga hadari kada su rika fita yawace-yawace, kada kuma mutane su rika fakewa karkashin bishiya don reshe na iya karyowa ya illata mutum in ma bai yi kisa ba kenan. Kada mutane su rika amsa waya lokacin da ake tsawa da walkiya. Masana na ta fadakarwa kan wannan. “
Bisa al’ada dai a jihar ta Kano a lokuta irin wannan ana samun kungiyoyi na aikin gayya wadanda kan dauki matakai na yashe magudanan ruwa don ba wa ruwa hanya wadatacciya ya wuce sai dai wannan dabi’a na raguwa a tsakanin al’umma, lamarin da masana kan muhalli ke ganin hakan babbar barazana ce ga makoma ta muhalli da ma shi kansa dan’Adam a muhallinsa.
Yusuf Bala Nayaya,Kano.
Leave a Reply