Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajanta wa wasu jami’an ofishin jakadancin Amurka biyu da ‘yan sandan Najeriya biyu da ke tare da su a wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Ogbaru ta jihar Anambra.
“Na yi matukar bakin ciki da jin labarin kisan da aka yi wa ma’aikatan ofishin jakadancin da ‘yan sandan mu da ke tare da su. A cikin wannan mawuyacin lokaci ga iyalan wadanda aka kashe, ofishin jakadancin Amurka da rundunar ‘yan sandan Najeriya, NPF, ina jajantawa al’ummar kasar kan wannan lamari mai ban tausayi,” inji shi.
Hakazalika an yi wa shugaba Buhari bayani game da kisan gillar da aka yi wa mutane da dama a gundumar Bwoi da ke karamar hukumar Mangu ta jihar Filato, da na wasu kauyuka kauyen Adaka da ke karamar hukumar Makurdi da kuma al’ummar Ijaha ta karamar hukumar Apa ta jihar Binuwai. .
Shugaban ya ce ya yi matukar bakin ciki da samun labarin wadannan munanan mace-mace kuma yana jajantawa iyalan wadanda lamarin ya shafa.
“Muna cikin alhinin ofishin jakadancin Amurka, rundunar ‘yan sandan Najeriya, da al’ummarmu a Filato da Binuwai, muna kuma jajircewa wajen kamo wadanda suka kai harin tare da gurfanar da su a gaban kotu. Allah ya ba iyalansu ikon jure rashin ,” in ji shugaban.
Leave a Reply