Jihar Kwara ta kasance jiha mafi kyau a fannin kiwon lafiya a duk yankin Arewa ta Tsakiya.
Jihar ta lashe babban birnin tarayyar Najeriya Abuja da sauran jihohin Arewa ta tsakiya inda ta samu matsayi na farko.
A wani taron da aka gudanar a Abuja ranar Laraba da daddare, jihar Kwara ta lashe lambar yabo ta kungiyar gwamnonin Najeriya, lambar yabo ta NGF’s Primary Healthcare Leadership Challenge award saboda ci gaban da aka samu a fannin a cikin shekaru hudu da suka gabata.
An cinye Kalubalen Jagorancin Kula da Lafiya na Farko na NGF a cikin 2019 a matsayin wani ɓangare na ‘Sanarwar Seatle’, wanda ke kimanta aikin gabaɗaya na isar da kiwon lafiya na farko ta amfani da alamomi kamar ‘tallafin gwamnati da sadaukar da kai, ingancin isar da sabis, haɓakawa a cikin ƙididdiga na kiwon lafiya da sakamako, shiga cikin al’umma da mallakarsu, da sauransu’.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Raji Razaq da babban sakataren hukumar kula da lafiya matakin farko na jihar Kwara, Dr. Nusirat Elelu ne suka karbi kyautar a madadin jihar.
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya kuma halarci bikin karramawar tare da wasu da dama masu rike da mukamai da tsofaffin gwamnoni daga sassan kasar nan.
Leave a Reply