Take a fresh look at your lifestyle.

Badakalar Kudin Haram: Kotu Ta Dage Shari’ar Wasu Kamfanoni Biyar

Abdulkarim Rabiu, Abuja

10 207

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, babban birnin Najeriya ta dage ci gaba da zamanta  zuwa ranar 19 ga watan Yunin 2023 domin gurfanar da Daraktoci a wasu kamfanoni guda biyar bisa samun su da laifin karkatar da kudaden gwamnati da kuma karya dokar bada kwantiragi ta gwamnati  dangane da kwangilar biliyoyin naira a kamfanin rarraba wutar lantarki na  na Najeriya TCN.

Manajan Daraktan Hukumar Raya Wutar Lantarki a yankunan karkara ta Najeriya, Ahmed Salihijo, da kamfaninsa na Velocity Nigeria Limited na daga cikin wadanda za a gurfanar da su a gaban kuliya.

Sauran kamfanoni hudun sun hada da Winslow Logistics, Equal Logistics, Sahams Crystal Investment da Antaser Nigeria Limited.

Mai shari’a James Omotoso ya tsayar da ranar Talata, bayan ya saurari lauyoyin biyu.

Donnington Limited ne ya shigar da karar a kan shugaban  Hukumar da kamfanoni hudu saboda rashin bayyana ayyukan kamfanoninsu kamar yadda aka kayyade a karkashin dokar haramta safarar kudade ta 2011 da kuma hukuncin da dokar ta tanadar.

Donnington ya yi imanin cewa, zai sanya kafar wando daya da babban mai shigar da kara na Najeriya wajen kafa wannan batu saboda rashin bin dokokin kasar da kamfanonin suka yi.

Ya ce, “Kasarmu ba za ta amince da saba wa dokar halatta kudaden haram ba da kuma rashin bin ka’idojin doka da Daraktocin kamfanonin dake neman kwangilar gwamnati suke aikata.”

Lauyan kanfanin Donnington Limited Mista Bala Sanga yayin da yake zantawa  da manema labarai, ya ce ya shigar da kara a kan kamfanonin biyar da cewa “kamfanonin sun karya tanade-tanaden doka”.

 

Abdulkarim Rabiu

 

 

10 responses to “Badakalar Kudin Haram: Kotu Ta Dage Shari’ar Wasu Kamfanoni Biyar”

  1. Please let me know if you’re looking for a writer for your site. You have some really good articles and I feel I would be a good asset. If you ever want to take some of the load off, I’d absolutely love to write some articles for your blog in exchange for a link back to mine. Please shoot me an e-mail if interested. Kudos!
    hafilat card balance check

  2. В динамичном мире Санкт-Петербурга, где каждый день кипит жизнь и совершаются тысячи сделок, актуальная и удобная доска объявлений становится незаменимым инструментом как для частных лиц, так и для предпринимателей. Наша платформа – это ваш надежный партнер в поиске и предложении товаров и услуг в Северной столице. Популярная доска объявлений

  3. купить оружие варфейс В мире онлайн-шутеров Warface занимает особое место, привлекая миллионы игроков своей динамикой, разнообразием режимов и возможностью совершенствования персонажа. Однако, не каждый готов потратить месяцы на прокачку аккаунта, чтобы получить желаемое оружие и экипировку. В этом случае, покупка аккаунта Warface становится привлекательным решением, открывающим двери к новым возможностям и впечатлениям.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *