Al’umar Gbagyi Na Abuja Sun Bayyana Goyon Bayan Su Ga Zababben Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shuaibu Nasir.
Al’ummar Kabilar Gbagyi da ke Abuja sun jaddada aniyarsu ta cigaba da bada goyon bayansu ga ganin an rantsar da sabon shugaban Najeriya, Alhaji Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, tare da yi masa fatan samun Nasara a mulkin sa.
Jagorar kungiyar Al’ummar da tun farko su ke goyon bayan takarar da Bola Ahmad Tinubu ya yi, Uwargida Hon. Dorathy Nuhu, ita ce ta bayyana hakan yayin bukin ranar Gbagyi na wannan Shekarar da ya gudana a Dandalin hadin kan kasa ( Unity Fountain ) da ke Birnin Abuja, fadar Gwamnatin Najeriya.
Hon Dorathy ta bayyana murnar ta a madadin daukacin al’ummar Gwarawa (Gbagyi) da ke cikin da wajen Najeriya, musamman ma mazauna Babban Birnin Tarayyar Abuja; “..wadanda suka shahara wajen kaunar zaman lafiya da saukar bakin da suka taru saboda nasarar da Zababben Shugaban kasar Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima suka samu a zaben shekarar nan ta 2023”. A cewar ta.
Haka kuma Uwargida Dorathy ta kara da cewa “a bana suna gudanar da bukin ne kafada da kafada da gangamin nisanta kabilar Gbagyin daga wasu gurbatattun baren mazauna Abuja da ke ikirarin kasancewarsu yan kasa ko Yan asalin Abuja, wadanda suka shigar da kara dan neman Kotu ta dakatar da rantsar dasabon Shugaban kasar Mai jiran Gado Alh Bola Ahmed Tinubu a ranar Ashirin da tara ga watan Mayun nan”.
A cewar ta, “wannan ma shi ne babban dalilinsu na ware rana guda inda suka fito fili don nuna godiyarsu da goyon bayan ga sabon shugaban na Najeriya Mai jiran gado, kana kuma sun yi hakan ne domin nesanta kansu daga wadanda suka shigar da Kara kotu bayan shan kaye a zaben, da nufin kawo targarda ga Shirin rantsar da sabuwar gwamnatin”.
A nashi jawabin, madugun kungiyar goyon bayan Bola Ahmad Tinubu (TSG), Mr. Tosin Adeyanju ya bayyana irin kwarin gwiwar da jagorar tafiyar Hon. Dorathy Nuhu ke basu na ci gaba da murnar samun nasarar gwanin na su, tare kuma da cewa za su ci gaba da wannan gangami tun daga yanzu har zuwa narar Litinin 29 ga watan Mayu 2023 ranar da za a rantsar da zababben Shugaban Kasar mu Alh. Bola Ahmed Tinubu.
Cov/Shuaibu
Leave a Reply