Take a fresh look at your lifestyle.

Hukumar USAID ta yi alkawarin dala miliyan 255 a Kenya don yakar fari

4 268

Hukumar raya kasashe ta Amurka, USAID, ta ce za ta bai wa Kenya dala miliyan 255 taimakon gaggawa da raya kasa don magance fari. KU KARANTA KUMA: Ebonyi: Hukumar USAID ta hada gwiwa da ‘yan jarida don inganta harkar lafiya Shugabar Hukumar ta USAID, Samantha Power ce ta bayyana hakan a ranar Juma’a, inda ta bayyana cewa, gwamnatin Kenya ta ce mutane miliyan 4.1 a yankin gabashin Afirka na fama da karancin abinci, sama da miliyan 3.8 a watan Maris din bana. Alkawarin bayar da tallafin ya zo baya ga dala miliyan 65 da USAID ta riga ta bayar a bana, in ji shugabar hukumar ta USAID Samantha Power. “Muna bukatar wasu kasashe su tashi tsaye su shiga tare da mu,” in ji ta, tana mai gargadin cewa matsalar abinci na iya yaduwa zuwa wasu fannoni kamar ilimi tun da yara masu fama da yunwa ba sa iya zuwa makaranta. Kawo yanzu gwamnati ta kashe kudi biliyan 12.6 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 106.28 don taimakawa mutanen da fari ya shafa amma tana da gibin sama da biliyan 15, in ji ministar kula da tsare-tsare na musamman Margaret Kobia. Mamayewar da Rasha ta yi wa Ukraine, wanda ya yi fama da matsalar samar da abinci a duniya, na kara addabar fari a Kenya da sauran yankin, in ji Power. Sama da mutane miliyan 50 ne ake sa ran za su fuskanci matsalar karancin abinci a bana a kasashen Djibouti, Habasha, Kenya, Somaliya, Sudan ta Kudu, Sudan da Uganda, in ji hukumar samar da abinci ta duniya a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da wasu hukumomi a ranar Juma’a.

4 responses to “Hukumar USAID ta yi alkawarin dala miliyan 255 a Kenya don yakar fari”

  1. если снится значит думает о тебе беременная
    теща во сне к чему снится видеть венчание в
    церкви
    молитва на благосклонность преподавателя на экзамене грибок
    ногтей и ног заговоры

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *