Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya shugaba Recep Tayyip Erdogan murnar nasarar da ya samu a zaben shugaban kasa bayan ya doke dan takarar adawa Kemal Kilicdaroglu a zagaye na biyu na zaben.
Shugaba Buhari ya ce sake zaben Erdogan na da kyau don kyautata dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Turkiyya.
“Ina maraba da sake zaben Erdogan, gwarzon dan takara na gaskiya da adalci a duniya kuma aminin Najeriya.
“A madadin gwamnati da al’ummar Najeriya, ina cewa barka da warhaka abokina kuma aminin Najeriya na gaskiya. Karkashin jagorancin ku, huldar da ke tsakanin kasashenmu biyu za ta bunkasa daga karfi zuwa karfi.
“Ina yi muku fatan sake samun nasarar zama ofis,” in ji shi.
Leave a Reply