Take a fresh look at your lifestyle.

‘Yan Najeriya Sun Yi Dakaru Zuwa Dandalin Eagle Square Domin Kaddamar Da Tinubu

0 174

‘Yan Najeriya sun fara tururuwa zuwa dandalin Eagle Square da ke Abuja, wurin da ake gudanar da bikin rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da misalin karfe 6:00 na safe agogon Najeriya ranar Litinin.

Hatta ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi da sanyin safiya bai hana mutane ba yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wurin taron.

Mafi akasarin hanyoyin da za a bi wajen taron daga sassa daban-daban na Abuja, jami’an tsaro sun toshe su bisa ga dukkan alamu su kare duk wani tabarbarewar tsaro.

Shiga wurin taron na da matukar wahala yayin da jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda, sojoji, hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, da jami’an tsaron farin kaya na Najeriya, NSCDC, ke ta tofa albarkacin bakinsu kan masu shiga wurin.

An shirya fara taron da karfe 10:00 na safe agogon Najeriya.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *