Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB, ta ce ba ta daukar ma’aikata a kowane ofishinta, haka kuma ba ta baiwa wani ko kungiya kwangilar yin hakan a madadinta ba.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka sanyawa hannu kuma ta mika wa Muryar Najeriya ta hannun mukaddashin daraktan hulda da jama’a na hukumar, Dr. Fabian Benjamin.
Hukumar JAMB a cikin sanarwar ta ce an ja hankalinta kan ayyukan da ba su dace ba na wata kungiyar daukar ma’aikata da ke aiki a Akure, jihar Ondo, a kudu maso yammacin Najeriya, inda ta ce an ba ta kwangilar daukar ma’aikata a madadinta.
Ta kuma ce kungiyar ta yi wannan ikirarin ne ta hanyar amfani da shafin sada zumunta na musamman.
Sanarwar ta ce, “Kungiyar, wacce ke aiki a karkashin “Akure Job and Business Advert Forum”, da ke Quarters 92 Alagbaka Estate, kusa da ofishin CBN, IBB Avenue, Akure, Jihar Ondo, tana amfani da sunan JAMB, ofishin Jihar Ondo. don tallata guraben aiki a matsayin sakatariya da na malamai a cikin Hukumar”.
“Hukumar, ta wannan furucin ne, tana ba jama’a shawara da su yi watsi da irin wadannan bayanai domin a halin yanzu ba ta daukar ma’aikata a wani ofishinta, haka kuma ba ta da wani ko wata kungiya da ta yi hakan a madadinta.
Sanarwar ta kara da cewa “Duk wanda ke yin kasuwanci da dandamalin da aka ambata a sama ko makamantansu, yana yin hakan ne bisa nasa/hadarin ta. Haka kuma, za a dauki tsauraran matakai na shari’a kan duk wanda aka samu da laifin aikata irin wadannan munanan ayyukan.”
Don haka hukumar ta shawarci jama’a da su yi taka-tsan-tsan da jiga-jigan miyagu masu son damfarar ma’aikatan da ba su da aikin yi domin duk sanarwar da hukumar ta bayar ana yin ta ne kawai ta hanyoyin da ta amince da su.
Leave a Reply