Take a fresh look at your lifestyle.

Kwamitin Aiyyuka Na kasa Ya Nada Zababben Sanata

0 96

Kwamitin ayyuka na kasa, NWC na jam’iyyar Social Democratic Party, SDP, ya nada zababben Sanata Ahmed Wadada domin ya hada jiga-jigan jam’iyyar a majalisar wakilai ta kasa ta 10.

 

Nadin na kunshe ne a wata wasika a Abuja ranar Asabar mai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar na kasa, Alhaji Shehu Gabam, da sakataren kasa, Dr Olu Agunloye.

 

Wadada zai wakilci mazabar Nasarawa-Yamma a majalisa ta 10.

 

Wasikar tana cewa: “Kungiyar NWC ta babbar jam’iyyarmu ta SDP, a taronta, ta yanke shawarar nada ku a matsayin shugabanta da kuma hada kan jiga-jigan ‘yan jam’iyyar SDP da aka zaba domin yin aiki a majalisun kasa da na jihohi a fadin kasar nan.

 

“Manufar wannan ita ce kawo dukkan zababbun ‘yan jam’iyyar Social Democratic Party zuwa ga manufa daya ta inganta hadin kai da manufofin jam’iyyar.

 

“Ana sa ran kwamitin zai kai ga samar da moriyar juna ga jam’iyyar da kuma ‘yan majalisar da suka zama babban matsayi na babbar jam’iyyar mu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *