Take a fresh look at your lifestyle.

Majalisa Za Ta Yi Kokarinta Don Waware Matsalar Tallafin Man Fetur: Hon. Al- Mustapha

Abdulkarim Rabiu, Abuja.

0 340

Majalisar Wakilan Najeriya ta dauki matakin nemo hanyar warware matsalar da ake fuskanta kan batun tallafin man fetur ta hanyar kafa kwamiti da zai gudanar da binkice a kan yadda akan tattalafin Man Fetur tun daga shekarar 2017 zuwa 2021.

Shugaban kwamitin, Dan Majalisar Tarayya Mai wakiltar Mazabar Wurno da Raba, Honarabul Ibrahim Almustapha Aliyu daya Jagoranci zaman kwamitin a Majalisar, ya bayyana cewa akwai shirye-shirye da tsare-tsaren da suke gudanar wa domin tabbatar an samu mafita a cikin lamarin.

Honarabul Ibrahim ya kara da cewa tun daga lokacin da aka kafa kwamitin a ranar 23 ga watan Juli, kwamitin ta fara tsare-tsare da gudanar da bincike a kan wadanda ke da ruwa da tsaki a kan harkar domin zakulo abin da yake matsalar.

Ya ce “ba wai mun fito ido rufe bane na neman masu laifi, amma duk wani dan kasa harkar mai tana damun shi domin ya kamata a sassautawa yan Kasa amma bai kamata a saka ido a bar abubuwa na tabarbarewa ba.”

“Kasa na neman Kudi domin a inganta harkar noma, harkar Ilimi, harkar sufuri, samar da ruwan sha da shinfida tituna, amma an Kasa gane inda aka dosa.”

“Wato duk abin da ake yi na gudanar da wata hada-hada kuma ya kamata a yi shi a bisa doka. Hukumar yin rajistar kamfanoni da kamfanin Man Fetur na kasa NNPC su suka san duk wadanda suka cancanta.”

“Sai wadanda suka yi hulda da su sun zo sun bamu bayanai, shi yasa sai NNPC da ta shiga hulda da su sun zo sun yi mana bayani domin ta yu abin da muke tunani ba shi ne ba.”

Acewarsa, mai yuwa tallafin ya amfani yan Najeriya ba tare da al-mubazaranci ba, ko hasara kamar yadda mutane suke hasashen hakan.

 

LADAN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *