Majalisar dattawa ta amince da bukatar da shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya gabatar na nada masu bada shawara na musamman guda 20.
Bukatar ta shugaba Tinubu na kunshe ne a cikin wata wasika da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanta yayin zaman majalisar a ranar Talata.
A cikin bukatar shugaban kasar bai lissafa sunayen mashawarta na musamman guda 20 da za a nada ba. Sai dai majalisar dattawan ta yi gaggawar amincewa da bukatar bayan an karanta wasikar.
Lawan ya ce a cikin gaggawa shugaban kasa ya samu tawagarsa da za ta yi aiki da su. Yace; “Saboda babu sunan masu ba da shawara na musamman, za mu amince da shi daga nan, muna jin cewa wannan wani abu ne na gaggawa.”
Bukatar ta zo ne kwanaki kadan bayan da shugaba Tinubu ya bayyana nadin kakakin majalisar wakilai mai barin gado, Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikatan fadarsa, da kuma tsohon ministan ayyuka na musamman, George Akume a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya.
A halin yanzu, Majalisar Dattawa ta 9 za ta yi zamanta na ranar Alhamis, 8 ga Yuni, 2023.
Leave a Reply