Kwamishinan Yan Sandan Jahar Neja Ya Rabawa Magada Kudi A Madadin Sifeta Janar Na Yan Sandan Najeriya
Nura Muhammad
Kwamishinan Yan Sandan Jahar Neja dake Arewa ta tsakiyar Najeriya Ogundele Ayodeji, psc ya raba naira miliyan ashirin da shida da dubu dari biyu da ashirin da bakwai da dari hudu da tara da kwabo sha bakwai (26,227,409.17) ga iyalan jami’an yan sandan da suka rasa ransu a yayin gudanar da aiki.
Wadanda da aka raba wa kudin su 15 ne da Kuma wasu 38 da suka sami rauni a yayin gudanar da ayyukan su amadadin sifeta janar din yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba.
An dai raba chakin kudin a ranar talatan nan a hedikwatan rudunar yan sanda dake Dutsen-kura a garin Minna fadar gwamnatin jahar Neja.
A cewar kwamishinanan yan sandan hakan wani bangare ne na taimakawa jami’an karkashin Shirin inshura na Group Life Assurance (GLA) ga wadanda suka rasa Rai, yayin da Kuma aka baiwa wasu 38 da suka sami rauni kudin shima a tsarin inshora na Group Personal Accident (GPA) domin kula da lafiyar su.
CP Ogundele Ayodeji psc, ya Kuma yiwa wadanda suka rasu addu’oin fatan rahama da kuma jajantawa iyalai da yan uwan su bisa rashin da suka yi, kana ya yiwa wadanda suka sami rauni fatan samun sauki.
Leave a Reply